Majalisar Jamus ta amince a tallafawa Girka

Image caption Shugabar Jamus, Angela Markel

Majalisar dokokin Jamus ta bai wa kasar izini ta fara tattaunawa kan yiwuwar bai wa Girka tallafi a karo na uku.

An dai yi zazzafar mahawara kan batun kafin 'yan majalisar suka amince da kudurin da gagarumin rinjaye.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce wannan batu ne mai sarkakiya ga dukkan bangarorin, to amma ta ce in ba hakan aka yi ba, kasar Girka za ta fada cikin wani mawuyacin hali.

Ministan Kudin Jamus, Wolfgang Schauble ya ce kasar za ta yi iya bakin kokarinta domin ganin an cimma nasara.

A bangare guda kuma ana ci gaba da tattaunawa kan batun shirin ceto tattalin arzikin Girkar na Yuro biliyan 80, wanda zai dauki watanni kafin a kammala.