Jami'an SSS sun saki Sambo Dasuki

Image caption Kanar Sambo Dasuki mai murabus

A Najeriya, jami'an hukumar tsaro na farin kaya SSS sun saki tsohon mai bai wa gwamnatin Najeriya shawara kan sha'anin tsaro Kanar Sambo Dasuki daga daurin talala na fiye da tsawon sa'o'i 24.

Wasu rahotanni sun ce jami'an hukumar ta SSS sun janye daga kawanyar da suka yi wa gidan Kanar Sambo Dasuki dake Abuja ne bayan sun karbe pasfo din sa da kuma wasu muhimman takardu.

Kanar Sambo Dasuki wanda ya nuna rashin jin dadin sa da hana shi zuwa sallar Idi da jami'an na SSS suka yi, ya sha alwashin kalubalantar abin da ya kira take mashi hakki a gaban kuliya.

Wasu rahotanni sun nuna cewa, saboda wasu matakai na diflomasiyya da Kanar Sambo Dasuki ya dauka kafin a sauke shi, gwamnatin Najeriya ta samu karbo kuaden da kasar Afirka ta Kudu ta kwace da aka je sayo makamai kasar bara.