Amurka- wutar daji a jihar California

Wutar daji a jihar California Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wutar daji a jihar California

Mahukunta a jihar California ta Amurka sun kwashe sama da mutane 300 daga sansanonin da ke fuskantar barazanar wata wutar daji.

Rahotanni sun ce wuatr dajin na tafiya ne cikin sauri.

Jami'an gandu dajin San Bernardino sun ce an aike da jami'an kashe gobara akalla dubu daya don shawo kan gobarar.

Babu dai wani rahoton samun jikkata kana babu wani gini dake cikin barazana.

Wata wutar dajin ta da ban kuma dake arewaci ta mamaye wata babbar hanya, inda ta tilastawa masu motocin barin ababan hawan su.

Motoci kalla 20 ne wutar ta yiwa ta'annati.