An sake bude shagunan Westgate a Kenya

Rukunin shuganan Westagate a birnin Nairobi na Kenya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rukunin shuganan Westagate a birnin Nairobi na Kenya

An sake bude rukunin kantunan kayan nan na Westgate dake birnin Nairobi na kasar Kenya, bayan da ya shafe kusan shekaru biyu a rufe.

Rufewar ta biyo bayan harin da wasu 'yan bindiga suka kai tare da hallaka jama'a da dama.

Masu sayayya sun yi layi a wajen harabar ginin, yayinda gwamnan Nairobi Evans Kidero ke kaddamar da sake bude kantunan.

An kuma dauki tsauraran matakan tsaro, inda aka rika yin binciken kwakwaf ga duk wanda zai shiga kantin.

Har yanzu dai, ba a gudanar da binciken da gwamnati ta sha alwashin yi ba, kuma wani kwamitin majalisar dokokin kasar ya soki abin da ya kira sakacin jami'an tsaro.

Wasu bidiyoyi da na'urorin sirri suka dauka a cikin shagungunan, sun nuna yadda wasu jami'an tsaro cikin kayan sarki suna 'yan sace sace lokacin da harin.

Mutane 67 ne suka mutu a harin da aka shafe kwanaki hudu ana bata kashi da 'yan kungiyar Alshabab dake da alaka da Al'Qaeda.