Za a sake bude shagunan Westgate a Kenya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ginin shaguna na Westgate

A Kenya, bayan kimanin shekaru biyu da kai wani mummunan hari a wani babban ginin shaguna a Nairobi, yanzu haka an shirya sake bude ginin na Westgate.

Mutane 67 ne suka mutu a harin da aka shafe kwanaki hudu ana bata kashi da 'yan kungiyar Alshabab dake da alaka da Al'Qaeda.

Za a sake bude ginin shagunan ne mako guda kafin ziyarar da shugaban Amurka Barrack Obama zai kai kasar, wani lamari da ake gani, mahukuntan Kenya suna da tabbaci ga matakan tsaro da suke dauka.

Har yanzu dai, ba a gudanar da binciken da gwamnati tasha alwashin yi ba, kuma wani kwamitin majalisar dokokin kasar ya soki abin da ya kira sakacin jami'an tsaro.

Wasu bidiyoyi da na'urorin sirri suka dauka a cikin shagungunan, sun nuna yadda wasu jami'an tsaro cikin kayan sarki suna 'yan sace sace lokacin da harin.