An sake gina 14 daga cikin wuraren tarihi a Mali

Ginin tarihin na Timbuktu a kasar Mali Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ginin tarihin na Timbuktu a kasar Mali

Majalisar Dinkin Duniya ta sake gina 14 daga cikin wuraren tarihi na Timbuktu da mayakan Islama suka lalata shekaru uku da suka gabata.

Mayaka masu tsattauran ra'ayin addinin Islama ne dai suka kai hari, tare da lalata gine-ginen da kayyakin tarihi a arewacin Mali a shekara ta 2012.

Darakta Janar ta hukumar raya al'adu ta Majalisar dinkin duniya UNESCO Irina Bokovi ta ce, ana daukar batun lalata kayan tarihi a matsayin wani babban laifin da ya shafi yaki.

A taron bikin kaddamar da gine-ginen, Ms Irina ta ce tana fatan kotun hukunta masu aikata laifuka ta kasa da kasa ICC, za ta bincika tare da hukunta wadanda suka lalata wuraren tarihin.

Gine-ginen wuraren bauta ne na musulmai tun a karni na goma sha biyar da kuma sha shida.

Wasu magina mazauna yankin ne suka gudanar da aikin sabunta gine-ginen, tun bayan da aka fatattaki mayakan a shekara ta 2013.