Buhari zai gana da Obama

Image caption Shugaba Buhari yana so Amurka ta taimakawa Najeriya wajen yaki da Boko Haram.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya isa birnin Washington inda zai gana da Shugaba Barack Obama.

Ana sa ran za su gana ne da misalin karfe hudu na rana a agogon Najeriya.

Jami'an fadar White House sun ce shugabannin biyu za su tattauna kan yadda za su hada kai domin yaki da kungiyar Boko Haram.

Dangantaka tsakanin Amurka da Najeriya ta yi tsami a lokacin shugabancin Goodluck Jonathan bisa zargin da ake yi wa sojin Najeriya na taka hakkin dan adam.

Shugaba Buhari ya sha alwashin kawar da matsalar cin hanci, kana ya dauki aniyar kwato kudaden da aka sace daga Najeriya aka boye a bankunan Amurka da Switzerland da sauran kasashen waje.