Janar Hlaing zai amince da sakamakon zaben Myanmar

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Janar Min Aung Hlaing

Shugaban rundunar soji a Myanmar ya ce zai amince da sakamakon zaben da aka shirya yi nan gaba kadan a cikin shekarar da muke ciki ko da kuwa 'yan adawa ne suka samu nasara.

Sai dai a cikin wata hira da yayi da BBC, Janar Min Aung Hlaing ya ce sojoji za su cigaba da taka rawa a harkokin siyasar kasar har sai an samu zaman lafiya da dai-daito da masu tayar da kayar baya a Myanmar.

Mr Haling ya cigaba da cewa da farko na yi amanna cewa zaben zai kasance sahihi wanda babu magudi a ciki, Wannan shi ne babban fatanmu.

Muna kokari muga mun taimaka an samu hakan.

Idan har hukumar zabe ta sanar da sakamako to zamu amince dashi ba bu ja.

Ana ganin cewa jam'iyyar Aung San Suu Kyi ce zata iya samun nasara a zaben da za ayi a watan Nuwamba mai zuwa.