Obama ya jinjina wa Buhari wajen yakar Boko Haram

Hakkin mallakar hoto Nigeria government
Image caption Obama ya ce Amurka za ta tallafawa Najeriya idan dai Najeriyar ba ta kauce hanya ba.

Shugaban Amurka Barack Obama ya ce Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya yana da tsari mai kyau na kawar da kungiyar Boko Haram da ma inganta tattalin arzikin kasar.

Mr Obama ya bayyana haka ne a ganawar da ya yi da Shugaba Buhari a fadar White House ranar Litinin.

Ya yi kira ga shugaba Buhari da ya yi amfani da karfin soji hadi da inganta rayuwar jama'a domin murkushe Boko Haram.

A cewar Obama, Amurka za ta tallafawa Najeriya idan dai Najeriyar ba ta kauce hanya ba.

Shugaban na Amurka ya roki takawaransa na Najeriya ya hada gwiwa da dukkan 'yan kasar domin ci gaban ta.

Ya kara da cewa Najeriya na da matukar kima a Afirka don haka duk abin da ya samu kasar zai yi tasiri a sauran kasashen da ke nahiyar.