Habre zai sake komawa kotu

Hakkin mallakar hoto
Image caption Tsohon shugaban Chadi Hissane Habre

Nan gaba kadan tsohon shugaban kasar Chadi Hissane Habre zai sake bayyana gaban kotun da take hukunta laifukan yaki a Senegal.

An dai fara sauraron karar ne tun a ranar litinin, sai dai Mr Habre wanda yaki amincewa da halaccin kotun, an fitar dashi daga kotun bayan da ya rika ihu, yana cewa shari'ar "shirme" ne kawai.

Alkalin kotun ya bayar da umarnin ya dawo kotun domin fuskantar wasu daga cikin mutanen da ya yi wa laifi a lokacin mulkin sa.

Ana dai zargin Mr Habre da bayar da umarnin kisan dubban mutane da azabtar da su a lokacin da yake mulki.

Shari'ar da ake yi masa wacce kungiyar kasashen Afirka ta shirya ita ce ta farko da ake yi wa wani tsohon shugaba a wata kasar da ba tasa ba.