Abin da Buhari ya rubuta a Washington Post

A ziyarar zuwa Amurka, Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya wallafa manufofin gwamnatinsa a jaridar Washington Post.

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da Buhari ya ce;

  • Hedkwatar rundunar sojojin Nigeria ta koma Maiduguri, inda manya manyan hafsoshin Nigeria za su zauna daga yanzu.
  • Yakin da zamu kaddamar a kan Boko Haram zai kasance cike da kalubale, za a samu nasarori da kuma koma baya, amma kada wani ya yi shakka a kan kudirinmu na kawar da ta'addanci daga Nigeria.
  • Wajibi ne gabanin mu nada ministoci, mu shimfida sabobbin dokoki na gudanar da ingantaccen mulki.
  • Rashin ingantancen tsari na gudanar da mulki ya sa jami'an gwamnati sun yi ta sama da fadi da kudaden gwamnati ba tare da an sa musu ido ba.
  • Ina neman hadin guiwar Amurka domin gano dala biliyan 150 da aka sace daga Nigeria aka boye a bankunan kasashen waje.
  • Rashin ingantaccen mulki a Nigeria na daga cikin dalilin da yasa aka kasa samun nasara akan kungiyar Boko Haram
  • Aiki na farko da ke gabanmu shi ne samar da ingantaccen mulki, na biyu samar da kwararrun jami'ai wadanda za su gudanar da ma'aikatu sannan na uku kwato kudaden da aka sace a karkashin gwamnatocin da suka shude domin amfanin 'yan Nigeria.
  • Muna bukatar kawayenmu su taimaka mana da horar da sojojinmu da kuma bamu bayanan sirri a yakin da muke da Boko Haram.
  • Na san an zabe ni domin kawo sauyi, sannan mutane sun kosa, amma kawo gyara ga Nigeria bayan shekarun daka shafe ana tabargaza ba zai samu ba a dare daya.