Ana zaben shugaban kasa a Burundi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Burundi, Pierre Nkurunziza

A ranar Talata ne al'ummar kasar Burundi suke kada kuri'unsu domin zaben shugaban kasa, duk kuwa da cewa masu hamayya sun sanar da kaurace wa zaben.

Zaben dai yana zuwa ne bayan kwashe watanni ana yin rikicin tun bayan yunkurin da wasu sojojin kasar suka yi na kifar da gwamnatin shugaba Pierre Nkurinziza a watan Mayu.

Rikicin ya samo asali ne tun bayan da Shugaba Nkurinziza ya sanar da aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugabancin kasar karo na uku.

Kasashen duniya sun yi ta kira ga kasar ta Burundi da ta dage zaben domin gudun barkewar yakin basasa, amma hakan ya ci tura.

Ko a daren ranar Litinin zuwa wayewar garin Talata an yi ta jin karar fashewar bama-bamai da bindiga a wasu yankunan Bujumbura, babban birnin kasar.