Ma'aikacin da ya rasu wajen ceton masu Ebola

Tulip Mazumdar, wakiliyar BBC ta fanin lafiya ta koma kasar Saliyo domin tantance gudunmowar Augustine Baker, ma'aikacin lafiya wanda ya mutu a yaki da cutar ta Ebola.

Image caption A lokacinda cutar Ebola ta yi tsanani, Augutine Baker ya kan shiga al'umomin da cutar ta fi kamari domin ya taimakawa yara wadanda su ka zama marayu sandiyar cutar Ebola

Hukumar da ke kula da kananan yara ta Majalisar dinkin duniya ta ce, yara sama da dubu 18 sun rasa iyayensu a yammacin Afrika sanadiyar cutar Ebola.

Sama da 8,000 na yaran suna Saliyo, inda ake samun raguwar masu dauke da cutar a watannin baya-bayan nan.

Sai dai kuma suna fuskantar kalubale wajen sake hada wasu marayun al'umominsu, kamar yadda na gani da na koma gidan marayu na St George wanda 'yan kasar Ingila ke kula da shi a Freetown babban birnin kasar, watanni shida bayan da ta kai ziyarata ta farko.

Wannan gida mai fanti kallar ruwan kwai, ba boyayye bane, kuma an kula da daruruwan yara wadanda iyayensu suka rasu sakamakon cutar Ebola tun barkewar ta.

'Babban Rashi'

Ina shiga, sai ma'aikatan kula da harkar lafiya wadanda ban hadu da su ba a ziyarar da na yi a baya ba su ka gaishe ni.

Mutumin da na hadu da shi shi ne Augustine Baker.

Ya mutu sakamakon cutar Ebola da dadewa kuma cutar ta yi sanadiya mutuwar matarsa, Margaret.

Yanzu yaransu uku sun zama marayun Ebola.

Image caption Ebola ta kashe dubban yara a Saliyo da Laberiya da kuma Guinea
Image caption A yanzu yaran Augustin suna karkashin kulawar kakarsu, Juliet

Isatu Kamara wani ma'aikacin lafiya a gidan maru inda Augustine ya yi aiki ya ce "Ya sadaukar da rayuwarsa yana yiwa yara aiki."

"Mun ji wannan mutuwar sosai. Yanzu yaransa sun zama marayu. Muna cikin bakin ciki sosai."

Yaran Augustine, da karamin cikinsu mai shekara daya suna karkashin kulawar kakarsu.

Na hadu da mahaifiyar Augustine a gidan marayun. Mutuniyar kirki ce kuma mai kima, amma kuma kamannin ta sun nuna alamun rashin kuzari da gajiya.

Juliet ta ce " Duk sanda na tuno da dana, a ko da yaushe sai nayi kuka. Mutuwar ta zo ne kwatsam. "Mutumi ne kamili."

Augustine ya suma ne a loakcin da ake wata ganawa a offishin marayun a watan Fabrairu. Bayan ya mutu, sai da aka killace cibiyar na tsahon mako uku. Abin godiya shi ne babu wanda ya kamu da cutar ta Ebola.

Augustine Baker da barnar da Ebola ta yi wa mutane

'Kin Amincewa'

Hukumar da ke kula da kananan yara ta Majalisar dinkin duniya ta kiyasta cewa yara dubu 8,619 sun zama marayu sakamakon Ebola a Saliyo.

Image caption A na gudun yaran da iyayen su suka rasu a sanadiyar cutar Ebola a al'ummominsu saboda suna ganin mai yuwa za su iya dawo musu da cutar
Image caption 'Yan uwan Augustine Baker suna matukar alfahari da irin rawar da ya taka a wajen yaki da cutar Ebola kafin ya mutu watan Fabrairu

Ta ce yawancinsu sun iya komawa cikin al'ummominsu kuma 'yanuwa suna kula da su.

Mma kuma mafi yawancin wadannan iyalan, wadanda suke fama da rashi suna fafitikar yadda zasu ciyar da mutanen da suka karu a iyalin.

A lokacin da na kai ziyarar karshe gidan marayun, marayu 50 ne ake kula da su. Yanzu akwai kusan 20.

Yayinda aka samu raguwar masu dauke da cutar zuwa kusan 10 a mako a Saliyo, an mayar da hankali daga nemo marayun Ebola zuwa tabbatar da samun kyakkyawar kulawa ga wadanda aka mayar da su al'umominsu.

Image caption A gina gidan marayun ne a shekarar 2004, kuma har barkewar cutar Ebola, cibiyar tana ceto yara marasa galihu

Sai dai har yanzu akwai zaman dardar tsakanin mutune da wadanda suka warke daga cutar ta Ebola, kamar yadda Isatu Kamara ta shaida min.

''Muna samun yara da yawa da 'yan uwansu ke gudun su, ana nuna musu kyama, musamman yaran da suka warke daga cutar Ebola''.

''Mutane na tsoronsu, ba su amince cewa yaran sun warke daga cutar ba, ba sa son taba su ko zama kus da su, dan haka su na nisantar yaran da inda suke''.

Irin wannan aiki shi ne abu na watannin karshe da Augustine Baker ya yi kafin mutuwarsa. Mahaifiyar augustine ta ce za ta tabbatar 'ya'yansa sun san jihadin da mahaifinsu ya yi wa kasar Saliyo.

'' Zan shaida musu abinda ya yi, za kuma su yi alfahari da shi''.