Boko Haram:Bankin duniya zai kashe biliyoyi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram sun yi barna sosai a arewa maso gabashin Nigeria

Bankin duniya ya sha alwashin kashe dala biliyan biyu da miliyan 100 wajen sake gina yankin arewa maso gabashin Nigeria da rikicin Boko Haram ya daidaita.

Wata sanarwa da kakakin shugaban Nigeria, Femi Adesina ya fitar, ta ce matakin ya biyo bayan tattaunawar Shugaba Buhari da gidauniyar Bill and Melinda Gates da kuma bankin duniya da kuma hukumar lafiya ta duniya-WHO a birnin Washington.

Sanarwar ta ce Shugaba Buhari ya ce sake gina matsugunan mutane kusan miliyan daya da 'yan Boko Haram suka raba da muhallansu na daga cikin abubuwan da ya fi bai wa mahimmanci a gwamnatinsa.

A bisa tsarin dai, bankin duniya zai kashe wadannan kudaden ne ta hannun Cibiyar Raya Kasashen Duniya wadda ke ba da bashi ga gwamnatoci a kudin ruwa mara yawa.

Shekaru 10 na farko, zai kasance babu kudin ruwa sai kuma kudin ruwa mara yawa a shekaru 30 masu zuwa.

Bankin duniya din kuma ya ce zai kashe kusan dala miliyan 300 a allurar rigakafi kan cutar Maleriya.

A yayinda gidauniyar Bill and Melinda Gates tare da hadin gwiwar gidauniyar Dangote domin kawar da cutar Polio daga Nigeria.