An gano maganin cutar mantuwa

Hakkin mallakar hoto SLP
Image caption Bincike ya nuna cewa mai fama da cutar zai iya samun sauki idan aka ba shi maganin da wuri.

Wani sabon bincike da aka yi ya nuna cewa an gano maganin-gwaji da zai hana ci gaban da cutar mantuwa ke yi.

Miliyoyin mutane ne ke fama da cutar, mai suna Alzheimer, a turance.

Binciken da kamfanin hada magunguna mai suna Eli Lilly ya yi ya nuna cewa idan aka bai wa mai fama da cutar maganin Solanezumab da wuri zai rage kaifin ciwon da kuma ci gaban da take yi da kimanin kashi uku cikin dari

Binciken da aka gudanar a shekarar 2012 bai yi tasiri ba.