Buhari ya yi watsi da auren jinsi daya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Buhari ya ce dokoki da al'adun Najeriya suna kyamar auren jinsi daya.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya yi watsi da batun auren jinsi daya.

Kakakin shugaban, Femi Adesina, ya ce an tabo batun auren jinsi guda a wajen taron da Shugaba Buhari ya yi ranar Talata a Amurka, amma Shugaba Buhari ya ce dokokin Najeriya da al'adun kasar suna kyamar luwadi da madigo.

Mr Adesina, wanda ya yi karin haske kan batun a shafinsa na Twitter, ya ce "an bijiro da batun auren jinsi daya a nan jiya (talata). Shugaba Buhari ya fito karara ya ce dokokin Najeriya da al'adunta na kyamar luwadi da madigo".

A shekarar 2014 ne 'yan Majalisar Dokokin Najeriya suka zartar da wata doka ta bukaci a aiwatar da hukuncin kisa kan duk matanen da aka kama sun yi auren jinsi, ko kuma wadanda ke da hannu a auren.