An kai harin bam a Marwa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wannan shi ne karo na biyu a cikin mako guda da ake kai hari a arewacin Kamaru.

'Yan kunar-bakin-wake guda biyu sun tashi bama baman da ke jikinsu a garin Marwa da ke lardin Arewa mai nisa na Jamhuriyar Kamaru.

Daya daga cikin su ya tashi bam din ne a kasuwar Central da ke garin.

Rahotanni na cewa mutane da dama ne suka mutu, sai dai har yanzu gwamnati ba ta bayar da adadin mutanen da suka mutu ba.

A garin na Marwa aka girke hedikwatar rundunar tsaron Kamaru da ke yaki da kungiyar Boko Haram.

Wannan shi ne karo na biyu a cikin mako guda da ake kai hari a arewacin Kamaru.