Nigeria: Gobara ta kashe mutane 100

Bututan mai a Najeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Bututan mai a Najeriya

Akallaa mutane 100 ne suka mutu sakamakon gobarar da ta tashi bayan fashewar wani bututun mai tsakanin jihohin Ogun da Lagos.

Wani wakilin BBC a yankin ya ce lamarin ya faru ne a dajin Alekpete a yankin Ikorodu da ke wajen birnin Lagos.

Ya ce mutanen na cikin kwasar ganimar man petur din da ke kwarara daga wani bututu da ya fashe ne lokacin da gobarar ta tashi.

Wasu bayanai na daban kuma sun ce gobarar ta tashi ne a lokacin da wasu daga cikin masu kwasar man suke kokarin tayar da injin kwale-kwalen su.

Sai dai kakakin rundunar hukumar tsaro ta Civil Defence a jihar Ogun, Abdulkareem Olanrewaju, ya shaidawa BBC cewa wani rikici ne ya kaure tsakanin masu kwasar ganimar lokacin da wani da ake zargin abin fashewa ne a hannunsa ya tayar da gobarar.

Rayukan jama'a da dama sun salwanta a yankunan kudancin Najeriyar sakamakon fashewar bututun man yayin kwasar ganimar.