"'Yan gudun hijira 44, 000 ne a Kamaru"

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban 'yan gudun hijra ne ke ficewa daga Najeriya saboda hare-haren Boko Haram.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce 'yan gudun hijirar da suka tsallaka daga Najeriya zuwa Kamaru sun kai 44,000.

Kakakin hukumar, Leo Dobbs ne ya bayyana hakan, yana mai yin gargadin cewa lamarin ya faru ne sakamakon sabbin hare-haren da 'yan Boko Haram ke kai wa a arewacin Najeriya.

A cewar sa, a 'yan makonnin da suka gabata, 'yan gudun hijira 30,000 ne a sansanin da ke Minawao, amma yanzu kusan kullum sai karuwa suke yi.

Ya yi kira a dauki kwakkwaran mataki na murkushe 'yan kungiyar ta Boko Haram domin mutane su ci gaba da zama a gidajensu.