An sayar da Financial Times a kan $1.3bn

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kamfanin ya mallaki Financial Times kusan shekaru sittin.

Masu jaridar Financial Times sun sayar da ita ga kamfanin watsa labaran Nikkei na kasar Japan a kan $1.3bn.

Kamfanin Pearson na Biritaniya ne ya mallaki jaridar tsawon kusan shekaru sittin.

Kamfanin ya ce sayar da Financial Times zai ba shi damar mayar da hankali wajen wallafa littattafai.

Kamfanin da ke buga Financial Times, yana wallafa wasu makaloli, kuma duk da ya sayar da jaridar zai ci gaba da mallakar kashi hamshin cikin100 na mujallar Economist , wadda ita ma yake wallafawa.