Jammeh ya yi wa maciya amanar kasa afuwa

Hakkin mallakar hoto

Shugaban Kasar Gambia Yahya Jammeh ya sanar da yin afuwa ga duk wanda ake zargi da cin amanar kasa daga shekarar 1994 zuwa shekarar 2013.

Ya yi wannan sanarwar ce a wani biki da aka shirya domin tunawa da shekaru 21 da yin juyin mulkin da ya kawo shi kan karagar mulki.

Shirin Afuwar ya hada da 'yan adawar da suke gudun hijira -- amma ba wadanda suka yi yunkurin hambarar da gwamnatinsa ba a wani juyin mulkin da bai yi nasara ba a watan Disambar bara.

Ba a dai san takamaimai yawan mutanen da za a saka ba.