Kerry ya yi martani ga Republican kan Iran

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yace tamkar mafarki ne ayi tunanin cewa akwai wata yarjejeniya da za'a iya cimma bayan wadda suka cimma.A wani taron jin bahasin jama'a na Majalisar Datijai a birnin Washington, Mr Kerry ya ce masu shiga tsakani daga manyan kasashen shida na duniya masu karfin fada a ji, sun tsara yadda zasu wargaza yadda Iran zata iya yin makamin nukliya

"Ya ce zabin da ke gabanmu shi ne ko mu cimma matsaya akan yarjejeniyar da zata tabatar cewa an takaita shirin nukliya ta kasar Iran ta hanyar sa mata ido cikin lumuna ko akasin haka".