Gwamnatin Kenya ta nemi CNN ta ba ta hakuri

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya

Gwamnatin Kenya ta nemi gidan talibijin na Amurka watau CNN ya bayar da hakuri kan taken da ya buga akan ziyayar da shugaba Obama zai kai kasar ranar juma'a, da ya ce zai ziyarci "cibiyar aikace aikacen ta'adanci".

Yan kasar Kenya sun dunga amfani da shafin twitter domin su yi Allah wadai.

Ministar harkokin waje ta Kenya, Amina Mohammed, ta fadawa BBC cewa ba ita kadai ce kasar da ke fuskantar matsalolin tsaro ba.

Ta ce ziyarar shugaba Obama ta nuna cewar kofar kasar a bude take domin gudanar da kasuwanci, kuma ta kasance kasar da sauran kasashe zasu iya koyi da ita.