'Yan Kenya sun soki CNN saboda Obama

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tashar talabijan din Amurka CNN, ta sha suka a shafukan sada zumunta na Kenya.

Masu amfani da shafukan sada zumunta da muhawara a kasar Kenya sun yi korafi a kan labarin da gidan talabijan din Amurka, watau CNN, ya wallafa wanda ke cewa Shugaba Obama zai ziyarci kasar da ke matsayin cibiyar tashe-tashen hankula.

Shugaba Obama zai ziyarci Kenya ranar Jumma'a mai zuwa.

Mau'du'in da suka kirkiro a shafin twitter watau #SomeoneTellCNN shi ne ya fi farin jini a shafukan sada zumuntar na Kenya, inda 'yan kasar su ka yi ta sukar gidan talabijin din.

Wani har ma yasauya musu suna a shafin twitter, ya maida su 'Confuse News Network', watau rudadden gidan labarai.

A cikin 'yan kasar ma wani ya kara da cewa su kasarsu ba ta tashin hankali ba ce, kasar cinikayya ce da mutanen kirki.

Wasu kuma suka janyo hankula a kan kashe-kashe masu alaka da launin fata da jami'an tsaro a Amurka ke yi, inda suke nuni da cewa ba a hakan a kasar Kenya.