Nkurunziza ya lashe zaben Burundi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Pierre Nkurunziza, ya lashe zaben Burundi.

Shugaban kasar Burundi, Pierre Nkurunziza, ya lashe zaben shugaban kasa a karo na uku.

Hukumar zaben kasar ce ta bayyana cewar Nkurunziza ya samu kaso 75 cikin 100 na kuri'un da aka kada ranar Talata.

Ana sa ran tabbatar da wannan sakamakon a cikin mako guda.

'Yan adawa dai sun kauracewa zaben, duk da cewa sunayen su na kan takardun kuri'un.

Agathon Rwasa ya samu kaso 19 cikin dari daga kuri'un da aka kada.

Kungiyoyin kasa-da-kasa sun soki zaben, inda suke zargin cewa ba a yi zaben bisa ka'ida ba.

An yi mamakin fitowar da mutane suka yi har kaso 73 cikin dari, domin ba a zaci za su fito haka ba.