Obama ya isa Kenya cikin tsauraran tsaro

Image caption Obama ya ce ziyarar tasa tana nuna da irin dukufar da Amurka ta yi wajen yaki da ta'addanci a gabashin Afirka.

Shugaba Barack Obama na Amurka, ya sauka a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, bisa tsauraran matakan tsaro da ba a taba ganin irinsu ba a kasar.

Kimanin 'yan sanda dubu goma aka baza a birnin.

An kuma rufe muhimman hanyoyi, yayinda jiragen yakin Amurka ke ta shawagi a sararin samaniyar birnin.

'Yan kasar ta Kenya sun bayyana ra'ayoyi mabanbanta game da ziyarar tasa.

Yayinda wasu ke yabawa, wasu kuma korafi suke yi game da takura su da suka ce an yi saboda samar da tsaro ga Obama.

Shugaba Obama wanda mahaifinsa dan asalin kasar ta Kenya ne, shi ne shugaban Amurka na farko da ya ziyarci Kenya, a lokacin da yake kan karagar mulki.

'Yan kungiyar Al shabab dai sun sha kai hare-hare a cikin kasar ta Kenya.

A hirar da ya yi da BBC kafin ya tafi Nairobin, shugaba Obama ya ce ziyarar tasa tana nuni da irin dukufar da Amurka ta yi wajen yaki da ta'addanci a gabashin Afirka, yana cewa Amurka za ta taka rawa wajen ganin cewa jarin da kasar China ke zubawa a Afirka ya amfani al'umar nahiyar.

Ya ce burinsa shi ne tabbatar da cewa kasuwancin ya amfani talakawan Kenya da na kasar Habasha ba wasu attajirai 'yan kalilan ba.