Shekara guda babu Polio a Nigeria

Polio in Nigeria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hukumomin lafiya a Najeriya sun yi ikirarin samun nasara akan cutar ganin an shekar ba'a kawo rahoton bullarta ba.

Hukumomin lafiya a Najeriya sun ce kasar ta cika shekara daya ba tare da samun wani da ya kamu da cutar shan inna wato Polio ba.

Hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki sun ce sun dauki matakai da yawa da suka sa aka kawo ga wannan matsayi.

Shugaban hukumar kula da harkokin lafiya a matakin farko a Nigeria, Dr Ado Muhammad, ya shaida wa BBC cewa idan nan da shekaru biyu ba a sake samun wanda ya kamu da cutar ba, hukumar lafiya ta duniya za ta ayyana kasar a matsayin wacce ta yi nasarar kawar da cutar ta Polio.

A baya dai Najeriya ta kasa cimma nasarar yaki da cutar shan innar sanadiyyar matsalolin da suka hada da kyamar allurar rigakafi da rashin kai wa ga yaran da ke kauyuka masu nisa, tare da matsalar sanya addini da siyasa a batun yaki da cutar shan innar.