Sabbin dabarun hare-haren Boko Haram

Hakkin mallakar hoto Yusuf Shettima
Image caption Farfesa Osinbajo ya bukaci kafafen watsa labarai su wayar da kan jama'a kan illar Boko Haram.

Mataimakin shugaba Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce wani rahoton sirri da suka samu ya nuna cewa 'yan kungiyar Boko Haram za su fara kai wa manyan mutane hare-hare.

Wata sanarwa da mai ba shi shawara kan watsa labarai ya fitar ta ce mambobin kungiyar ta Boko Haram za su fara yin shiga irin ta baban-bola domin zubar da shara mai dauke da bam a gidajen manyan mutane.

A kwanakin baya ne mataimakin shugaban na Najeriya ya kai ziyara arewa maso gabashin kasar domin jajanta musu kan hare-haren da Boko Haram ke kai wa a yankin.

Farfesa Osinbajo ya bukaci kafafen watsa labarai su zage-dantse wajen wayar da kan 'yan kasar kan irin dabarun da Boko Haram ke amfani da su domin kai hare-hare.

Wasu alkaluma sun nun cewa kungiyar ta kashe fiye da mutane 17, 000 tun da ta kaddamar da hare-hare a shekarar 2009, sanna ta raba miliyoyin mutane da muhallansu.