'Sojojin Nigeria sun kwato garin Dikwa'

Image caption Ana ci gaba da dauki ba dadi da 'yan kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Nigeria

Cibiyar nan da ke samar da bayanai a madadin hukumomin tsaron Najeriya, ta fitar da wata sanarwa da ke cewa rundunonin sojin Najeriya na sama da na kasa sun yi nasarar kwato garin Dikwa na jihar Borno.

Garin Dikwa dai a baya na hannun mayakan Boko Haram.

Sanarwar ta kara da cewa an yi amfani da jiragen sama samfurin Alpha Jet, da jirgin leken asiri wajen lalata wasu tungaye uku, da ke da manyan bindigogin kakkabo jiragen sama.

Hakan ne ya bayar da dama ga sojojin kasa suka shiga suka kame garin ba tare da wata turjiya mai yawa ba.

Sanarwar ta kuma kara da cewa, ana ci gaba da aikin bincike don kakkabe burbushin 'yan Boko Haram da suka rage a yankin.