Obama zai bude taron harkokin kasuwanci

Image caption 'Yan Kenya sun yi wa Obama kyakyawar tarba

Shugaba Obama zai bude wani taron koli kan harkokin kasuwanci a ranarsa ta farko ta ziyarar da ya ke yi a gabashin Afirka.

Ana tsammanin zai yi kiran a kara yunkuri na ganin an dakile cin hanci da rashawa , sannan zai yabawa kananan 'yan kasuwar Kenya.

Mr Obama zai kuma kai ziyara domin tunawa da wadanda aka kashe a wani harin bom da aka kai kan ofishin jakadancin Amurka dake Nairobi, sannan zai gana da Shugaba Uhuru Kenyatta domin su tattauna abubuwan dake tsakanin kasashen biyu

Ga alamu tattauwar za ta maida hankali ne akan yunkurin da Kenyan take yi na murkushe ta'addanci, a yanayi na barazanar da kasar ke fuskanta daga mayakan kungiyar al-Shabab

Amurka dai na taimakawa Kenyan a yakin da take yi da 'yan kungiyar, kuma ta kashe jagororin kungiyar da dama a farmakin da aka kai musu, da kuma hare- haren da jirage marasa matuka suka kaddamar