Bom ya kashe mutane 16 a Damaturu

Harin bam a jihar Yobe Najeriya Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Harin bam a jihar Yobe Najeriya

Akalla mutane 16 ne suka rasa rayukansu sannan wasu 46 suka jikkata sakamakon harin kunar-bakin-wake da aka kai a bakin kasuwar birnin Damaturu, da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya.

Harin ya faru ne da safiyar Lahadi lokacin da 'yan kasuwa ke fara gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Jami'an tsaro sun killace wurin tare da bukatar 'yan kasuwa da su rufe shagunansu saboda zaton da ake yi akwai wani bam din da aka dasa a kasuwar.

Babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, amma ana danganta irin wadannan hare-hare da kungiyar Boko Haram wadda ke ikirarin kafa daular musulunci a arewacin Nigeria.

Wanann hari shi ne na 3 da aka kai birnin na Damaturu cikin kasa da mako biyu, kuma dukkan hare-haren na kunar bakin wake ne da aka kai babban masallacin Idi da safiyar Sallah karama.

Sai kuma wani harin na daban da wasu mutane suka kai a wurin binciken ababen hawa, akan babban titin Maiduguri zuwa Damaturu.

Tuni dai gwamnatin jihar ta yi tur da harin.