APC ta gana da majalisar wakilai a Najeriya

Hakkin mallakar hoto national assembly
Image caption Majalisar dokokin Najeriya

Yayin da 'yan majalisar wakilai a Najeriya ke dawo wa bakin aiki a ranar Talatan nan, shugaban jam'iyyar APC mai mulki, Cif Odigie Oyegun ya gana da jagorori majalisar domin lalube bakin zare kan rikicin shugabancin da yaki ci yaki cinyewa a zauren majalisar, a daren Litinin.

Sai dai kuma kawo yanzu ba bu wani cikakken bayani kan matsayar da aka cimma a yayin ganawar, amma wani dan majalisa wanda ya tattauna da BBC ya ce idan an jima ne jagororin majalisar za su sanar da matsayar, a zauren, a lokacin zaman'yan majalisar.

Tun da farko dai 'yan majalisar da shugaban jam'iyyar sai da suka gana da shugaba Muhammadu Buhari a yammacin Litinin din, a inda ya umarce su da su je su sasanta su kuma sanar da shi yadda ta kaya.

'yan majalisar ta wakilai dai sun kwashe makonni biyar suna hutu.

Kafin tafiyar su hutun dai zauran ya samu kansa a cikin halin yamutsi na jagoranci, al'amarin da wasu ke ganin ya tilastawa 'yan majalisar rufe zauren domin lalubo bakin zaren.

Rikicin dai mai nasaba da jagoranci ya samo asali ne sakamakon zargin da wasu 'yan majalisar suka yi cewa shugaban majalisar, Yakubu Dogara ya bujurewa umarnin uwar jam'iyyar APC kan bukatar da ta aike masa ta ba wa wasu wadanda ta zaba domin cike wasu mukamai a majalisar da suka hada da na shugaban masu rinjaye.

Bangarori daban-daban sun tayin kokarin sasantawa amma al'amarin ya ci tura.