'Yar Bobby Brown ta rasu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Bobbi Kristina Brown da mahaifiyarta Whitney Houston

Bobbi Kristina Brown, 'yar marigayiya mawakiya a Amurka, Whitney Houston ta rasu tana da shekaru 22.

Wakiliyar iyalan gidan Bobby Brown, ta ce Kristina ta rasu ne a ranar Lahadi.

Tun a cikin watan Janairu, Bobbi Kristina Brown ta ke jinya bayan da aka same ta kwance rai-kwakwai-mutu-kwakwai.

Ta kasance 'ya daya tal ga marigayiya Whitney Houston da kuma mawaki Bobby Brown.

A shekara ta 2012 ne Whitney Houston ta mutu a wani otal a Los Angeles.