Kurdawa sun zargi dakarun Turkiya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dakarun Turkiya sun ce za su fatattaki kungiyar IS

Wata kungiyar sa kai ta Kurdawan arewacin Syria ta yi zargin cewa Turkiya na kai wa mayakanta hari kusa da iyaka.

Ta ce tankuna yaki na kasar Turkiya sun bude wuta a wuraren da ke karkashin ikon Kurdawa kusa da garin Jarablus, kuma an lalata mata daya daga cikin motocinta kusa da garin Kobane.

Turkiyar ta amsa kai harin kuma ta ce za ta binciki zargin.

A wani bangaren kuma Amurka da Turkiya sun amince su yi aiki tare domin kawar da kungiyar IS daga arewacin Syria.

Jami'an Amurka sun ce burinsu shi ne a samar da wani yanki a kusa da kan iyaka da Turkiya domin tabbatar da tsaro.