Shin aikin dare yana da illa?

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Mutane masu aikin dare na fuskantar kalubale

An gabatar da bincike bila'adadin a shekarun baya-bayan nan da suke nuna cewa aikin dare na da matukar illa ga lafiya. Sarah Montague ta rubuta cewar masu aikin dare yana jefa masu yinsa cikin fargaba.

An debi shekaru ina tashi cikin tsakiyar dare domin tafiya wajen aiki. Hakan ne ya sa nake samun damar gabatar da shirin 'Today' - kuma ina farin ciki da hakan.

Amma ina yawan mamaki ko ana iya samun matsala a gaba. Ko tashin da nake a lokacin da jikina ke bukatar na koma bacci zai iya jawo min illa ta din-din-din da za a iya sauya shi in an samu isasashen bacci da daddare?

Ina daya daga cikin mutane miliyan 3.5 da ke aikin dare Biritaniya. Yawancinsu suna shafe sa'o'i masu yawa suna aiki ko kuma su shafe tsawon dare suna aiki.

Ba ga masu aikin dare kawai hakan ke faruwa ba. Shekaru 50 da suka gabata yawanci manya na samun bacci sa'o'i takwas ne kacal. Amma yanzu mafi yawan mutane na baccin sa'o'i shida da rabi ne kawai.

Da yawa daga cikinmu na ganin kamar bacci bashi da amfani.

A duk lokacin da agogona ya buga da misalin karfe 3.25 na talatainin fare, na kan yi wa kaina alkawarin rama bashin baccina daga baya. Gani nake kawai kamar gajiya ce ta fi damuna.

Amma bacci yana da matukar muhimmanci kamar shakar iska da cin abinci. Da daddare ne kwakwalwarmu ke bukatar hutawa daga ayyukan da muka shafe tsawon yini muna yi.

Kuma a lokacin ne jikinmu ke samun irin hutun da yake bukata.

'Binciken Masana'

A yanzu dai mun gano cewa koda masu aikin dare sun samu isasshen bacci -- to basu yi shi a lokacin da ya dace ba.

A koda yaushe muna hasashen cewa jikinmu zai saba da yanayin aikinmu na dare, amma kamar yadda daya daga cikin kwararru kan bincike a harkar bacci a Biritaniya, Farfesa Russell Foster na jami'ar Oxford, ya ce "sakamakon da aka samu daga bincike daban-daban da aka gudanar ya nuna cewa baccin rana ba zai iya maye gurbin na dare ba kuma jiki ba zai saba da haka ba."

Kuma hakan na nufin akwai yiwuwar masu aikin dare na tsawon lokaci su kamu da manyan cututtuka kamar ciwon suga ko ciwon zuciya ko kuma cutar daji.

Masana kimiyya sun yi amanna cewa duk wanda yake tafiya wajen aiki da misalin karfe 4 na asuba-- kamar yadda nake yi, to kuwa zai ta tafka shirme a yayin aikin tamkar wanda ya ke cikin maye.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Rama bacci da rana ba zai maye gurbin baccin dare ba

Ba wai mutum zai kasance cikin zallar maye bane, amma dai mutum zai yi ta fama da tunanin abin da ya fi dacewa mutum ke yi ne.

A lokacin ne za mu yi ta tunanin abin da ya kamata mu karanta ko mu rubuta sa'o'i biyu kafin mu fara watsa shirye-shirye.

Wani babban bincike da aka gudanar da Amurka ya yi ta bin diddigin ma'aikatan jinya mata 75,000 wadanda suke aikin dare tsawon shekaru 22.

Binciken ya nuna cewa daya daga cikin mutane goma da ke aikin dare na tsawon shekaru shida suna mutuwa da wuri.

Ba wai kawai cutar da kanmu muke yi ba, wasu ayyukan da muke yi ma na saka wasu daban cikin hadari ne.

Na tattauna da wani wanda yake aikin share-share da daddare.

Maimakon yin bacci idan ya koma gida, ya ce da zarar ya yi bacci fita yake aikin tuka babbar mota kuma. Ya kan yi haka a kwanaki shida cikin mako daya, bacci sa'o;i uku kacal yake yi.