Shin wa ya kashe gawurtaccen zakin Zimbabwe?

Hakkin mallakar hoto
Image caption Akwai ratsin bakin gashi a wuyan Zakin

Gwamnatin Zimbabwe ta fara neman wani mutumi ruwa-a-jallo bisa zarginsa da kashe wani gawurtaccen zaki a gidan ajiye namun dajin kasar.

Ana zargin mutumin da bai wa masu kula da gidan ajiye namun dajin Hwange cin hancin sama da $50,000 domin ya kashe zakin mai suna Cecil the lion.

Wani mai kula da namun dajin Johnny Rodrigues ya shaida wa BBC cewa an harbi zakin ne da kwari-da-baka da kuma wata karamar bindiga, sannan aka yanka namansa.

Zakin, mai shekaru 13, yana cikin zakunan da masu ziyartar gidan namun dajin suka fi so.

Zimbabwe kamar sauran kasashen Afrika, na fama da hana farautar damun daji ba bisa ka'ida ba wanda hakan ke jawo karewar namun daji.

Mista Rodrigues shi ne shugaban wata kungiya da ke rajin kare hakkin dabbobi namun daji, ya ce amfanin da aka yi da kwari da baka wajen kashe zakin ya nuna wata sabuwar hanya ta gujewa kama masu laifin.

Ya shaida wa shirin BBC Newsday cewa "ba tare da wani kwarmato ba wannan ya nuna yadda za ka iya yin duk abinda ka ke so ta haramtacciyar hanya."

'Kafa tarko'

Kazalika, zakin wanda ke da ratsin baki a gashin da ke wuyansa bai mutu nan take ba kuma sai da aka bi bayansa fiye da sa'o'i 40 bayan nan aka harbeshi da bindiga, in ji Mista Rodrigues.

An daurawa Zakin wata alama da ke gano dukkan abin da ke faruwa da shi wadda wata kungiyar bincike a jami'ar Oxford da ke Biritaniya ta samar.

Mista Rodrigues ya kara da cewa kisanna da ban tausai kwarai.

Yana mai cewa "Zaki ne da baya damun kowa. Yana daga cikin dabbobin da ke da kyawun gani.

"An yaudari Zakin ne ta hanyar kafa masa tarkon fita daga cikin gidan namun dajin, wadda ita ce hanyar da mafarautan ke bi wajen cimma burinsu," in ji Rodrigues.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Zaki ne da baya damun mutane kuma yana daga cikin dabbobi masu kyawun gani.

An kama masu kula da gidan namun dajin guda biyu kuma in har aka tabbatar da cewa mafaraucin dan kasar Sifaniya ne, to za a tona masa asiri kan abinda ya aikata, a cewar Mista Rodrigues.

Yanzu haka dai za a kashe 'ya'yan Cecil guda shida, saboda sabon sarkin dawan ba zai bar su su girma ba ta yadda har zai samu damar kusantar zakanyar uwarsu.

Mista Rodrigues ya ce "haka abin yake, haka dabi'ar dabbobin take."