An kashe gawurtaccen Zaki a Zimbabwe

Image caption Zakin, mai shekaru 13, yana cikin zakunan da masu ziyartar gidan namun dajin suka fi so.

Gwamnatin Zimbabwe ta fara neman wani mutum ruwa-a-jallo bisa zargin kashe wani fitaccen zaki a gidan ajiye namun dajin kasar.

Anar zargin mutumin da bai wa masu kula da gidan ajiye namun dajin Hwange cin hancin sama da $50, 000 domin ya kashe zakin mai suna Cecil the lion.

Wani mai kula da namun dajin Johnny Rodrigues ya shaida wa BBC cewa an harbi zakin ne da kwari-da-baka da kuma wata karamar bindiga, sannan aka yanka namansa.

Zakin, mai shekaru 13, yana cikin zakunan da masu ziyartar gidan namun dajin suka fi so.