Kamaru za ta kara dakaru don yakar BH

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tuni dakarun Kamaru 7,000 suke filin daga don yakar Boko Haram

Jamhuriyar Kamaru na shirye-shiryen tura karin dakaru 2,000 zuwa lardin arewa mai nisa, bayan hare-haren kunar bakin wake uku da mayakan Boko Haram suka kai Maroua a makon da ya gabata.

An dauki matakin ne bayan da hukumomi a garin Doula suka haramta amfani da burka a kokarin da ake yi na karfafa tsaro.

An kuma haramta bara da tallace-tallace.

Hukumomin sun kuma dauki matakan rufe wasu masallatai da makarantun islamiyyoyi a lardin arewa mai nisan tare da sanya dokar hana zirga-zirga daga karfe shida na yamma.

mai magana da yawun hukumomin tsaro na kasar Kanal Didier Badjeck, ya tabbatar da kara yawan dakarun a lardin arewa mai nisa amma bai yi wani karin bayani kan hakan ba.

'Hare-hare mafi muni'

Hare-haren kunar bakin wake da aka kai garin Maroua a makon da ya gabata sun kasance mafi muni da mayakan Boko Haram suka taba kaddamarwa a jamhuriyar Kamaru.

Tuni dai kamaru ta tura dakaru 7,000 karkashin hadin gwiwar dakarun yankin tafkin Chadi da suka hada da na Chadi da Nijar da kuma Najeriya domin yakar kungiyar Boko Haram.

A ranar Laraba ne ake sa ran shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyara Kamaru inda zai gana da shugaba Paul Biya kan yadda za a hada karfi don shawo kan matsalar.