Dan Ghana zai shafe shekaru 10 a kurkuku

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kotun ta sami mutumin da laifin yunkurin kisan kai

Wata kotu a Accra , babban birnin kasar Ghana ta yanke hukuncin daurin shekaru goma a kan wani mutum da yayi ikirarin cewa yana kokarin hallaka shugaban kasa John Dramani Mahama.

Ranar Lahadin da ta wuce ne aka kama Charles Antwi da bindiga a cocin da shugaban kasar ke zuwa da iyalinsa.

Shugaban kasar dai ba ya cocin a ranar da lamarin ya auku.

An ambaci mutumin a kotu yana cewa ya dauki matakin ne domin ya karbe iko daga hannun shugaban kasar.

Tuni dai wasu suka fara nuna shakku game da koshin lafiyar mutumin, da kuma mamaki kan saurin yanke hukuncin.