Ko za a iya samar da fasahar amfani da batir?

Image caption Wayar salula kirar Motorola

Shugaban kamfanin da ke kera wayar salula kirar Motorola Rick Osterloh ya ce zai so ace an samar da fasahar amfani da batir.

Sai dai kuma shugaban kamfanin ya ce ya yi amanna wannan yunkuri zai dauki dogon lokaci kafin a samar dashi.

Kazalika Mr Rick Osterloh ya ce kamfanin sa ma zai dauki dogon lokaci kafin ya samar da wayar da batirinta zai shafe mako guda bai kare ba.

Shugaban kamfanin Motorolan ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya ke kaddamar da sabbin wayoyin salular da kamfanin ya kera.

Daga cikin wayoyin salular da aka kera sabbi akwai samfurin Moto X models wadanda sun kasance wayoyin komai da ruwanka ne wadanda ke saurin caji ba tare da bata lokaci ba.

Sauran wayoyin da aka kera akwai kirar Moto G mai saukin farashi.

Kamfanin dai ya samar da wadannan sabbin wayoyin ne domin ya yi gogayya da sauran kamfanonin kera wayoyin salula a kasuwannin duniya.

Kamfanin kera wayoyin na motorola ya shahara wajen kera wayoyi na zamani.