Tsohon minista a Nigeria 'ya sace $6bn'

Hakkin mallakar hoto Nigeria government
Image caption Buhari ya mika kokon bara ga Obama kan masu cin hanci a Nigeria

Gwamnan jihar Edo ya yi zargin cewa minista a tsohuwar gwamnatin Nigeria da ta wuce ya sace dala biliyan shida.

Adams Oshiomole ya ce jami'an gwamnati a Amurka ne suka sanar da Shugaba Muhammadu Buhari a lokacin ziyarar da ya kai a Washington a makon da ya gabata.

Akwai zarge-zargen cin hanci da karbar rashawa a kan gwamnatin Goodluck Jonathan da ta sha kaye a hannun 'yan adawa.

A cikin watan Mayu ne Buhari ya hau karagar mulki abin da ya kawo karshin jagorancin jam'iyyar PDP wacce ta shafe shekaru 16 a kan mulki.

Mr Oshiomhole, wanda ke cikin tawagar Buhari a Washington bai bayyana sunan ministan da ya sace kudin ba.

A lokacin ziyarar Buhari a Washington, shugaban ya bukaci Amurka ta taimaka wajen kwato dala biliyan 150 da aka sace daga Nigeria aka kai bankunan kasashen waje.