kungiya tana son kare hakkin yara akan intanet

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Kungiyar tana yin kira da a kare hakkin yara akan intanet

Wata kungiya mai rajin kare hakkin kananan yara, mai suna 'iRight' ta kaddamar da wani kamfe na ganin cewa yara za su iya goge abubuwan da suka sanya a shafukan intanet.

Wasu daga cikin burin kungiyar dai ta 'iRight' sun hada da ba wa yara kanana 'yancin gyara ko kuma goge abin da suka sanya a intanet ba tare da sun wahala ba.

Kungiyar dai ta 'iRight' tana son ta zaburar da masana'antu wajen aiki tare da gwamnati domin kare hakkokin kananan yara da matasa dangane da abin da ya jibanci hada-hadarsu a kafar intanet.

Bugu da kari, kungiyar tana son da mutane su rinka kawar da kai daga abubuwan da yaran suka aika a kafar ta intanet.

Sannan kuma a rinka sanya yara a hanya domin fadakar da su hanyar da za su alkilta kudinsu wajen yin amfani da intanet din.

Tuni dai kamfanoni da dama da suka hada da Barclays bank da NSPCC da kamfanin shari'a na Schillings duk sun rattabawa wannan kamfe hannu.

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Wasu kamfanoni har sun rattaba hannu akan kamfe din

Shi ma Minista mai kula da harkokin intanet na Birtaniya, Baroness Shields yana daya daga cikin masu marawa wannan kamfe baya.