An hana mata sanya hijabi a Diffa

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A baya ma dai hukumomin jihar sun sanya dokar hana amfani da burka

A Jihar Diffa ta Jamhuriyar Nijar, hukumomi sun sanar da dokar hana sa hijabi ga mata tun daga yanzu har zuwa wani dan lokaci.

Hukumomin sun ce an dauki matakin ne da nufin magance matsalar hare-haren kunar bakin-wake da ake fuskanta, musamman yadda akan yi amfani da wasu mata sanye da Hijabi.

Malamai a jihar sun ce sun gamsu da dokar bisa la'akari da yanayin dar-dar da ake ciki a fadin jihar.

Ko a baya ma gwamnatin jihar ta Diffa ta yi hani da sanya burka ga mata sakamakon karuwar hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram a sassan jihar.

Jihar Diffa dai na daya daga cikin jihohin da 'yan kungiyar Boko Haram suka mayar karkatacciyar kuka a jamhuriyar Niger.