Israi'la ta aikata 'laifukan yaki' a Gaza

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane da dama sun rasu sakamakon rikicin

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta ce akwai ''kwakkwarar shaida'' cewa Isra'ila ta aikata laifukan yaki yayinda take mai da martani kan cafke daya daga cikin jami'anta lokacin wani tashin hankali a Gaza.

Kungiyar ta ce lugudan wutar da aka shafe kwanaki uku ana yi kan yankuna mai tarin jama'a, ya hallaka Palasdinawa a kalla 135.

Sojojin Isra'ilar sun kaddamar da abin da rahoton na Amnesty International ya kira gagarumin hari a zirin Gaza .

Sai dai Isra'ilar ta yi watsi da rahoton da cewa ya baiwa bangare daya fifiko.

An shafe kwanaki 50 a tashin hankalin tsakanin watan Yulin bara zuwa Agusta kafin a tsagaita wuta.