Kamfanin jirgin Kenya ya yi asarar $250m

Image caption 'Yan yawon bude ido sun kaurace wa Kenya saboda tsoron ebola da Al-shaabab.

Kamfanin jiragen saman Kenya na fama da matsalar kudi bayan da ya yi asarar $250m a shekarar kudi ta 2014/2015.

Wannan shi ne karon farko da kamfanin ya yi asarar da ta kai wannan adadi.

Kamfanin ya dora alhakin wannan asara ne a kan karuwar da masu gogayya da shi a gabashin Afirka suka yi da kuma kaurace wa Kenya da masu yawon bude idanu suka yi.

Tsoron da ake yi a kan yiwuwar kai hare-hare daga kungiyoyin masu tayar da kayar baya da kuma barkewar da cutar Ebola ta yi a kasashe uku na yammacin Afirka sun sa masu yawon bude ido suna jan-kafa wajen kai ziyara a gabashin Afirka.