Masar: An yi harbi a ofishin jakadancin Nijar

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masar na fama da hare-hare daga masu tayar-da-kayar-baya.

Hukumomi a kasar Masar sun ce wasu 'yan bindiga sun bude wuta a kan jami'an tsaro a wajen ofishin jakadancin Jamhuriyar Nijar da ke kasar.

Lamarin ya yi sanadiyar mutuwar wani mutum da raunata mutane uku.

Wata sanarwa da ma'aikatar cikin gida ta kasar ta fitar ranar Laraba ta ce an kai harin ne da misalin karfe daya na dare bayan an rufe ofishin da yankin Giza na birnin Alkahira.

An bayyana cewa harbin da cewa irin na harbi-ka-ruga.

Babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, koda yake kasar ta Masar na fama da hare-haren masu tayar-da-kayar-baya, cikin su har da masu alaka da kungiyar IS.