Oni na Ile-Ife ya rasu

Hakkin mallakar hoto wiki
Image caption Oba Okunade Sijiwade

Rahotannin daga garin Ile-Ife na jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya na cewa Basaraken gargajiyar nan na kasar yarabawa, Oba Okunade Sijiwade, wanda shi ne mai rike da sarautar Oni na Ife ya rasu a daren ranar Talata.

Makusantan mamacin -- wadanda suka sanar da rasuwar -- sun ce Oba Sijiwade, mai shekaru 85, ya rasu ne a wani asibiti da ke Biritaniya bayan ya yi jiyya.

Basaraken dai ya kwashe shekaru 35 a kan karagar mulki bayan hawa kan kujerar ta Oni a shekarar 1980.

Oba Ounade ya kasance na hannun damar tsohon sarkin Kano, marigayi Alhaji Ado Bayero.