Microsoft ya fitar da manhajar windows 10

Image caption Microsoft ya fitar da sabuwar manhaja

Kamfanin Microsoft mai kera manhajojin Kwamfiyuta, ya fitar da wata sabuwar manhaja mai suna windows 10, wadda za a bai wa masu amfani da manhajar sa kyauta.

Sabuwar manhajar za ta yi aiki ne a na'urorin kwamfiyuta da wayoyin salula da sauransu.

A hirarsa da BBC -- shugaban kamfanin na Microsoft Satya Nadella ya ce: "Wannan sabuwar manhaja wani babban ci gaba ne ga kamfaninmu, da ma harkar kwamfiyuta baki daya."

Kamfanin na Microsoft dai na fuskantar koma bayan cinikin kwamfiyutoci samfurin PC, kuma kasuwanci na samun habaka ne a bangaren wayoyin salula inda kamfanin ba shi da tagomashi.