Kalaman Cameron sun jawo ce-ce-ku-ce

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption David Cameron ya kira 'Yan ci-rani da "Farin-dango."

Kalaman da Firai ministan Biritaniya David Cameron ya yi a kan 'yan ci-ranin da ke kokarin shiga kasar inda ya kira su da "farin-dango", ya tayar da jijiyoyin-wuya.

Hukumar 'yan gudun hijira ta Biritaniya ta ce kalaman nasa wulakanta bil adama ne.

Firai ministan -- wanda yanzu haka yake wata ziyyara a Viyatnam -- ya yi maganganun ne lokacin da yake bayyana ra'ayinsa a kan rikicin birnin Calais na Faransa mai tashar jiragen ruwa, inda daruruwan 'yan ci-rani a karo na uku suka yi kokarin bi ta hanyar jirgin kasa ta karkashin ruwa a kokarin su na shiga Biritaniya.

Mista Cameron ya ce Biritaniya ba za ta zama tudun-mun-tsira ba ga 'yan ci-ranin da ke zuwa daga Calais, za kuma a tabbatar da tsare iyakokin Biritaniya.

Wani babban jami'i Peter Sutherland, ya zargi 'yan siyasar Birtaniya a kan yadda suke mayar da martani kan lamarin 'yan ci-rani ta hanyar nuna kyamar baki.