Rabin masu mu'amala da intanet suna kan Facebook

Image caption Mutane biliyan 1.49 ne suke amfani da Facebook a karshen watan Yuli

Rabin mutanen da suke ta'ammali da intanet a duniya suna shiga manhajar sada zumunta ta Facebook, akalla sau daya a duk wata.

Kamfanin ya ce yawan mutanen da suke shiga shafin na sada zumunta akalla a kowane wata ya tasamma zuwa kaso 13 cikin dari.

Yawan masu amfani da Facebook din a tsawon watanni uku, daga watan Mayu zuwa karshen watan Yuli sun kai biliyan 1.49 a fadin duniya.

Saboda haka yawan mutanen ya kai rabin kiyasin mutane biliyan uku da ke mu'amala da intanet a duniya.

Kamfanin ya ce mutane a kasar Amurka suna kashe minti daya daga cikin kowane mintuna biyar da suke da shi, a kan kafar sada zumunta ta Facebook din.

Hakan yasa kamfanin yana samun kudin shiga masu matukar kauri da yawansu ya kai dala biliyan 4.4 kwatankwacin fan biliyan 2.6.

Tallace-tallace ta kafar su ne suka fi kawo kudaden shigar.

Image caption Kusan kowa yana amfani da kafar Facebook

Mark Zuckerberg, mai shekaru 31 kuma dan asalin Amurka tare da abokansa guda hudu ne suka kirkiri kafar sada zumuntar ta Facebook, a shekarar 2004.